Kasashen G7 za su kara taimaka wa Ukraine
May 13, 2022Birtaniya ta bayyana cewa dole ne a dafa wa Ukraine da karin manyan makamai na yaki, haka da kakaba wasu karin takunkumai kan Rasha, a yayin da ita kuwa Faransa ta bayyana goyon bayan kungiyar NATO face sai Ukraine ta yi nasara a yakin da take da Rasha.
Kungiyar Tarayyar Turai ta da dauki alkawarin bada karin kudade Euro miliyan 500 ga Ukraine. Sai dai da yake mayar da martani a yayin wata ziyarar da ya kai a Tadjikistan, ministan harkokin wajen Rasha Sergueï Lavrov ya zargi tarayyar Turai da kai ruwa rana a rikicin da kasar ta ke da Ukraine.
Rashar dai na cigaba da yi wa Ukraine barin wuta ta sama da kasa, inda ko a wannan Jumma'ar ma'aikatar tsaron kasar ta ce ta kai wasu jerin hare-hare da maiamai masu linzami kan wata matatar mai a yankin Poltava da ke gabashin Ukraine din tare da lalata dumbin runbun tsimi na man fetur.