Gagarumin garanbawul a gwamnatin Saudiyya
December 28, 2018A karkashin garanbawul din an nada ministan kudi Ibrahim al-Assaf a matsayin sabon ministan harkokin waje.
A baya dai an tsare Ibrahim al Assaf yayin dirar mikiyar da yarima Mohammed bin Salman ya kaddamar a bara na yaki da cin hanci, a yanzu zai maye gurbin Adel al Jubair wanda aka mayar da shi matsayin mashawarci kuma karamin minista a ma'aikatar harkokin waje.
Haka nan kuma sarkin ya nada yarima Abdullahi bin Bandar bin Abdulaziz ya maye gurbin yarima Miteb bin Abdullah a matsayin shugaban rundunar tsaron kasa.
Garanbawul din dai na zuwa ne yayin da gwamnatin Saudiyyar ke kokarin dakile matsin lambar da ta ke fuskanta daga kasashen duniya game da kisan dan jaridar nan Jamal Khashoggi a ofishin jakadancin Saudiyya a Istanbul a watan Oktoba.
Sabbin nade naden dai za su taimakawa Yarima mai jiran gado Mohammed Bin Salman rike madafan iko kasancewar yawancin wadanda aka nada din mutane ne na hannun damansa.