Gallant: "Mun kashe ko jikkata fiye da rabin mayakan Hamas"
July 10, 2024A Lokcin da yake jawabi a zauren majalisar dokokin Isra'ila ta Knesset, Yoav Gallant ya yaba abin da ya danganta da nasarori masu yawa da rundunar kasar ta samu a kan Hamas, a daidai lokacin da rikicin ya shiga wata na goma duk da kokarin shiga tsakani da kasashen duniya ke yi don a tsagaita bude wuta. Sojojin na Isr'ila dai na ninka hare-hare a sassa da dama na Zirin Gaza tare da karfafa farmaki a tsakiyar birnin a kwanakin baya bayan nan.
Karin bayaniZa a koma teburin neman tsagaita wuta a Gaza:
Sai dai zahirin abin da ke faruwa ya yi hannun riga da bayanin da gwamnatin Isra'Ila ta yi a farkon watan Janairun 2024, inda ta sanar da cewa ta kammala rusa duk cibiyoyin soji na kungiyar Hamas. Wata majiya da ke da kusanci da masu shiga tsakniya ta nuna cewar shugabannin hukumar leken asiri ta CIA da na Isra'ila na kan hanyar zuwa birnin Doha domin tattaunawa batun tsagaita bude wuta da Hamas da aka kasa cimma matsaya a kai.