1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gambiya: Shugabannin Afirka na shirin halartar biki

Salissou Boukari
January 12, 2017

Shugaban kasar Benin Patrice Talon, ya ce yana tsammanin zai kasance tare da Shugaba Alassane Ouattara a ranar 19 ga wannan wata a birnin Banjul, domin halartar bikin rantsar da sabon shugaban kasar Gambiya.

https://p.dw.com/p/2Vg5w
Der Präsident von Benin Patrice Talon
Shugaban kasar Benin Patrice TalonHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Shugaban na Benin da ke wata ziyara a kasar Cote d'Ivoir, ya ce su na masu nuna farin cikinsu ga jin wasu kalamman shugaba Jammeh da ke nunin cewa, yana fatan ganin an samun mafita a wannan rikici. A wani jawabi da ya yi ta kafoyin yada labarai na kasar, Shugaba Yahya Jammeh ya soki shishigin da ya ce wasu kasashe na yi wa batun kasar ta Gambiya, inda kuma ya yi fatan ganin an walwale wannan rikici ta hanyar ruwan sanyi.

A Laraba ce dai ta kamata tawagar kungiyar ECOWAS a kalkashin jagorancin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta ziyarci birnin na Banjul domin tattaunawa da Shugaba Jammeh, amma kuma aka mayar da wannan tattaunawa ya zuwa ran Juma'a 13 ga wannan wata na Janairu.