Gangamin bukatar ɗage zaɓe a Angola
August 25, 2012Babbar Jam'iyyar adawa a ƙasar Angola ta yi kira da a ɗage gudanar da zaɓen ƙasa na ranar 31 ga watan Augusta da wata guda. Hakan acewarta zai bada daman tabbatar da adalci da gyaran kura-kuran da yanzu ya mamaye dokokin zaɓen.Yaƙin neman zabe a karo na biyu tun bayan yaƙin basasar shekaru 27a Angola dai, kasar Afirka ta biyu mai albarkatun man petur, na fuskantar matsaloli. A juma'a mai zuwa ce dai al'ummar Angolan zasu zaɓi 'yan majalisar wakilai, kana shugaban jam'iyyar data fi rinjaye zai kasance shugaban kasar. Shugaban babbar Jam'iyyar adawa ta UNITA a Angola Isaias Samakuva, ya faɗawa manema labaru a birnin Luanda cewar, akwai kura kurai na rashin ƙwarewar hukumar zaɓen kasar, ayayin da katalandan na jam'iyyar MPLA mai mulki, zai jagoranci maguɗi a harkokin zaɓen na Juma'a. Yace suna muradin ganin an gudanar da zaɓe, amma idan hukumar zaɓen bata shirya gudanarwa ba, ana iya bata karin makonni domin ta shirya sosai. A wannan asabar din ce dai jam'iyyar adawar ta UNITA tta kira gangamin adawar kasa baki ɗaya, domin tilastawa hukumar zaɓen kasar gyara kura kurai da suka mamaye dokokin zaɓen.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Saleh Umar Saleh