1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gangamin bukatar ɗage zaɓe a Angola

August 25, 2012

Jam'iyar Adawa a Angola ta kira gangamin bukatar gyaran kura kuran dokokin zaɓe.

https://p.dw.com/p/15wa5
DSC_2793.JPG Titel: Mendes de Carvalho eröffnet Wahlkampf der Oppositionspartei CASA-CE Schlagworte: Wahlen, Wahl 2012, Angola, Politik, Wahlkampf, CASA-CE, Opposition Ort: Luanda, Angola Fotograf: Quintiliano dos Santos Datum: 31.07.2012 Beschreibung: Die neu formierte Oppositionspartei CASA-CE feiert vor ihrer Wahlkampfzentrale in Luanda den Wahlkampfauftakt am 31. Juli. Am 31. August 2012 finden in Angola Parlamentswahlen statt, zum ersten Mal tritt die Partei CASA-CE (Convergência Ampla de Salvação de Angola - Coligação Eleitoral) an. Es spricht Almirante "Miau" André Mendes de Carvalho, Admiral im Ruhestand und Sohn des prominenten Mitglieds der Regierungspartei MPLA , Mendes de Carvalho “Uanhenga Xitu”.
Hoto: Quintiliano dos Santos

Babbar Jam'iyyar adawa a ƙasar Angola ta yi kira da a ɗage gudanar da zaɓen ƙasa na ranar 31 ga watan Augusta da wata guda. Hakan acewarta zai bada daman tabbatar da adalci da gyaran kura-kuran da yanzu ya mamaye dokokin zaɓen.Yaƙin neman zabe a karo na biyu tun bayan yaƙin basasar shekaru 27a Angola dai, kasar Afirka ta biyu mai albarkatun man petur, na fuskantar matsaloli. A juma'a mai zuwa ce dai al'ummar Angolan zasu zaɓi 'yan majalisar wakilai, kana shugaban jam'iyyar data fi rinjaye zai kasance shugaban kasar. Shugaban babbar Jam'iyyar adawa ta UNITA a Angola Isaias Samakuva, ya faɗawa manema labaru a birnin Luanda cewar, akwai kura kurai na rashin ƙwarewar hukumar zaɓen kasar, ayayin da katalandan na jam'iyyar MPLA mai mulki, zai jagoranci maguɗi a harkokin zaɓen na Juma'a. Yace suna muradin ganin an gudanar da zaɓe, amma idan hukumar zaɓen bata shirya gudanarwa ba, ana iya bata karin makonni domin ta shirya sosai. A wannan asabar din ce dai jam'iyyar adawar ta UNITA tta kira gangamin adawar kasa baki ɗaya, domin tilastawa hukumar zaɓen kasar gyara kura kurai da suka mamaye dokokin zaɓen.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Saleh Umar Saleh