1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gargaɗi akan Tazarcen shugaban Senegal

June 23, 2011

Turai da kuma 'yan adawa a Senegal sun yi Allah wadai da yunƙurin da gwamnatin Senegal ke yi na sauya tsarin mulkin ƙasar.

https://p.dw.com/p/11i2n
Kantomar manufofin ƙetare na EU Catherine AshtonHoto: AP

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta bayyana damuwarta dangane da shirin yiwa tsarin zaɓen Senegal gyaran fuska, gabannin zaɓen ƙasar da zai gudana a watan Febrairun shekara mai zuwa. Kantomar kula da manufofin ƙetare ta ƙungiyar Catherine Ashton, ta ce shirin gwamnatin ƙasar na ƙoƙarin ganin cewar an sake zaɓen shugaba Abdoulaye Wade da kashi 25 daga cikin 100 na yawan kuri'u da za'a kaɗa, na buƙatar gudanar da ƙuri'ar jin ra'ayin jama'ar ƙasar. Ashton ta ce gyaran kundin tsarin mulkin ƙasar game da zaɓen shugaban ƙasa a wannan gajeren lokaci gabannin zaɓen, zai iya haifar da illa ga tsarin zaɓen shi kansa, wanda zai iya jagorantar ƙalubalantar sakamakonsa. Kantomar ta ce, kamata yayi a gudanar da kowane gyaran kundi, bisa ga ra'ayin al'ummomin ƙasar ta Senegal, domin tabbatar da sahihin zaɓe cikin adalci. A yau ne dai jam'iyyun adawa da ƙungiyoyin farar hula na Senegal ɗin suka shirya gudanar da zanga-zanga, adaidai lokacin da majalisar dokokin ƙasar ke mahawara kan yiwa kundin tsarin mulkin gyarar fuska.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Zainab Mohammed Abubakar