1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Gazawar rundunonin kiyaye zaman lafiya

Schwikowski Martina MAM
December 24, 2024

Samar da dakarun wanzar da zaman lafiya a kasashen Afirka da ke fama da yaki a nahiyar na fuskantar suka da caccaka iri-iri, bisa zargin rundunonin da gaza tabuka abin kirki wajen tabbatar da wanzuwar zaman lafiya.

https://p.dw.com/p/4oY87
Hoto: MONUSCO/Xinhua/picture alliance

 Batun rundonin wanzar da lafiya a nahiyar Afirka lamari ne da ke bukatar garambawul don aiwatar da shi ba tare karkata ga wani bangare na rikicin ba, kamar yadda kwararru a fannoni da dama na rayuwa a Afirka ke hannunka mai sanda a kai, sakamakon yadda matsalolin tashe-tashen hankula ke kara ruruwa a sassa dabam-dabam na Afirka. Dr Jakkie Cilliers shi ne shugaban kwamitin amintattu na cibiyar nazarin harkokin tsaro ta ISS da ke Afirka ta Kudu, ya nuna cewa tilas ne a kwance rigiza a sake dauri, don bijiro da tsare-tsaren da za su kai ga cimma nasarar abin da aka sanya a gaba, idan har da gaske ake: ''A fili take karara matakan dakile rikice-rikice da ake amfani da su ba sa biyan bukata, su kan su al'ummar nahiyar Afirka suna da laifi a kai, ko da yake akwai bukatar samun agaji daga kasashen waje, ta hannun Majalisar Dinkin Duniya. Wannan ce ta bai wa dakarun hayar kasar Rasha na  Wagner damar samun kafar shigowa nahiyar, tare ma da sauran kungiyoyi da ke kara haifar da ruruwar wutar gaba tsakanin Amurka da Rasha da China da kuma Turai, da ma na kwana-kwanan nan wato Hadaddiyar Daular Larabawa daga Gabas ta Tsakiya da kuma Turkiyya. Wani abu da ke kara dagula rikici a Afirka kuma shi ne yadda yadda kasashen nahiyar ke gaza hanzarin yayyafa ruwa ga duk wani rikici a cikin su har sai sun bari ya gagari sulhuntawa tun farkon faruwarsa''.

Demokratische Republik Kongo | UN Blauhelme nach Kämpfen mit Rebellengruppe M23
Hoto: Djaffar Sabiti/REUTERS

A 'yan shekarun nan an fuskanc ijuyin mulkin sojoji a wasu kasashen Afirka kamar su Mali da Chadi da Sudan, sai Burkina Faso da Guinea da kuma Jamhuriyar Nijar, yayin da aka yi yunkurin juyin mulkin hambarar da gwamnatocin kasashen Habasha da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kuma Guinea-Bissau. Ga kuma zaman tankiya a yankin kahon Afirka musamman ma tsakanin Habasha da Somaliya kan yankin Somaliland da ya yi ikirarin ballewa daga Somalia. Haka zalika har yanzu an gaza cimma masalaha kan yakin basasar Sudan da ya lakume rayukan dubban mutane da raba miliyoyi da gidajensu. Wani yunkuri na baya bayan nan na shirya zaman  da aka yi tsakanin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kongo da RUwanda ya ci tura, don samun damar dakile rikicin 'yan tawayen M23.

UN Peacekeepers | Bangladeschische Soldaten der Mission der Vereinten Nationen in der DR Kongo (MONUSCO)
Hoto: AFP via Getty Images

To sai dai duk da wannan koma baya da ake fuskanta a fannin kokarin warware tashe-tashen hankula don samun  zaman lafiya Mai dorwa a nahiyar Afirka, akwai wasu bangarori da ke samun tagomashi, in ji Alex Vines, babban daraktan kula da al'amuran Afirka a cibiyar Chatam House ta birnin London: '' Hanyoyin warware fadace-fadace na da fadi tamkar yadda rikice-rikicen ke da fadi, a don haka maimakon bin turba daya wajen magance matsalolin da suka dabaibaye yankin, kamata ya yi a fadada tunani a kan batun. Ko da yake ba lallai duk hanyoyin laluma su haifar da nasara ba, wannan dai tsari ne da ke bukatar agaji ta fuskoki da dama, ko da bayan tsayar da yakin''. Wasu alkaluma da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, sun nuna cewa kashi 42 cikin 100 na yarjeniyoyin zaman lafiya a duniya an kulla su ne a nahiyar Afirka,  tsakanin rikicin kasa da kasa ko kuma na cikin  gida.