1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghani: kofar sulhu a bude take ga Taliban

Ramatu Garba Baba
February 3, 2018

Shugaban kasar Afghanistan Ashraf Ghani ya bude kofar sulhunta rikicin da ke tsakaninsa da 'yan Taliban matikar suka ajiye makamai bayan shafe shekara da shekaru suna kai ruwa rana da bangaren da ke mulki.

https://p.dw.com/p/2s5Si
Ashraf Ghani Sicherheitskonferenz Kabul
Hoto: Reuters/O.Sobhani

Shugaban ya sanar cewa kofa a bude take na tattaunawa da mayakan da suka amince su ajiye makamai don samun zaman lafiya a kasar da ke ci gaba da fama da ayyukan kungiyoyi na masu tayar da kayar baya. Sai dai ya ce ko kadan wadanda ke da hannu a zubar da jinin da ake samu a kasar ba su da wannan dama,

Shugaban ya ci gaba da cewa duk da shirin na neman zaman lafiya hakan ba zai sa su zuba ido su bar mayakan da ke tafka ta'asar ayyukan ta'addanci su ci gaba da cin karensu ba babbaka ba. Ya fadi hakan ne a yayin jawabinsa gaban malaman addinin Islama a Kabul babban birnin kasar.

Kungiyar Taliban da ake zargi da kai akasarin hare-haren da suka yi sanadiyar rayukan mutane da dama na yakar dakarun sojin kawance da aka jibge a Afghanistan don kafa ta su gwamnatin daidai da tsari na shari'ar Islama. Mutane fiye da dari ne suka mutu a hare-haren bama-bamai da aka kai a cikin watan Janairu a sassan kasar.