Amirka ta fusata da gibin kasafin Jamus ga NATO
April 2, 2019Talla
Wannan mataki dai na daga cikin batutuwa masu sarkakiya da ke haifar da tsamin dangantaka tsakanin Berlin da Washington. Matakin na Jamus dai na zuwa ne yayin da kungiyar kawancen tsaro ta NATO ke shirin bikin cika shekaru 70 da kafuwa.
Ko da yake Washington ta amince da hujjojin da Jamus ta gabatar cewa ba za ta iya biyan bukatun NATO na karin kashi biyu cikin dari na abin da kasar ke samu a shekara har nan da 2024 ba, lamarin bai zo mata da dadi ba, kasancewar ko da kashi daya da digo biyar cikin dari da Jamus din ta yi alkawarin bayarwa ya faskara.