Sabon yunƙurin Isra'ila na gina matsugunan Yahudawa
July 30, 2015Talla
Isra'ila dai ta ƙwace iko da waɗannan yankuna ne tun a shekara ta 1967 yayin yakin Gabas ta Tsakiya. Har kawo yanzu dai Falasdinawa na yin ikirarin cewar wannan yanki mallakinsu ne da za su kafa ƙasar kansu a wajen. Tuni dai Amirka ta nuna matukar damuwarta a kan wannan sabon kudiri na Isra'ila wanda ka iya fuskantar tirjiya daga al'ummomin ƙasa da ƙasa. Dama Isra'ila ta jima ta na barazanar gina sababbin matsugunan Yahudawa a wannan yanki da suke taƙaddama a kansa ita da Falasɗinu wanda kuma al'umomin ƙasa da ƙasa ke nuna damuwarsu da kuma adawarsu a kan yunƙurin nata wanda suke cewar ya na iya ƙara ta'azzara rikicin da ke takanin Isra'ilan da Falasɗinu.