1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gobara a asibiti a Senegal

Abdourahamane Hassane
May 26, 2022

Wata gobar da ta tashi a wani asibitin dake a yammacin Senegal a garin Tivaouane ta kone jarirai 11 kurmus a lahira.

https://p.dw.com/p/4BtzD
Senegal Tivaoune | Elf tote Babies nach Feuer auf Kinderstation
Hoto: Seyllou/AFP

Gobara ta faru ne a sakamakon dameji da wutar lantarkin asibitin ta yi,wanda nan da nan dakunan asibitin suka kama da wuta. Gwamnan yankin Demba Diop ya ce an yi kokarin ceto jarirrai guda uku. Shugaba Macky Sall,wanda yanzu haka yake yin rangadi a cikin kasashen waje, ya wakilta ministansa na harkokin cikin gida zuwa birnin na Tivaouane cibiyar 'yan darikar Tijaniya domin isar da ta'aziyarsa.