1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Google ba ya kan komawa aiki a China

Gazali Abdou Tasawa
August 17, 2018

Shugaban Kamfanin Google Sundar Pichai ya sanar a wannan Juma'a cewar batun da ake na shirin komawar kamfanin aiki da kasar China yana matakin nazari ne kawai a yanzu.

https://p.dw.com/p/33Jig
China Google Office in Beijing
Hoto: picture-alliance/dpa

Shugaban kamfanin Google ya ce matsayin kamfanin game da al'amurran da ke wakana a alakar sa da China shi ne cewa suna nazarin ne kawai kan yadda za su yi aiki da kasar a nan gaba amma basu yanke hukunci ba tukunna. 

Kalaman shugaban kamfanin na shafin matambayi ba ya bata sun biyo bayan sukar da ma'aikatan kamfanin suka yi kan shirinsa na fara amfani da wata sabuwar manhaja da za ta rika boye bayanai game da 'yancin dan Adam da addini a Chaina, suna masu cewa matakin zai sa a rika kallon kamfanin a matsayin mai mara wa kasar China baya wajen take hakkin 'yan kasar na samun cikakkun bayanai game da duniyar da suke rayuwa a cikinta. 

Shekaru takwas da suka gabata ne dai kamfanin na Google ya fice daga kasar ta China bayan da ya ki amincewa da dokokin kasar masu neman tauye 'yancin dan Adam.