Guguwa ta janyo asarar rayuka a kudancin Afirka
March 19, 2019Talla
Bayan ficewar guguwar da ake yi wa la'akabi da sunan Idai wada ke tafe da iska mai karfin gaske hade da ruwan sama wace ta ratsa kasashen kudanci na Afirka. Masu aiko da rahotannin sun ce ruwan sama da ake ci gaba da shatatawa kamar da bakin kwarya na yin baranaza ga rushewar wasu madatsun ruwa a yanki. Guguwar wace ta share garuruwa da dama a Mozambik da kuma gabashin Zimbabuwe kawo yanzu ta kashe mutane 182.