1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gurbatar muhalli a Bodo Najeriya

Muhammad BelloJanuary 7, 2015

Kamfanin hakar danyan mai na Shell da ke aikinsa a Najeriya ya ce zai biya diyyar Fam na Ingila miliyan 55 ga al'ummomin kauyen Bodo da ke yankin Nija Delta a Tarayyar Najeriya bisa gurbata musu muhalli.

https://p.dw.com/p/1EGOc
Ölverschmutzung im Ogoni NDelta
Hoto: DW/M. Bello

Bayan takaddamar da kamfanin ya dade yanayi na kin biyan kudaden a karshe ya amince, abunda al'ummar yankin suka ce sun yi murna da hakan matuka. Kungiyar kare hakkin dan Adam ta duniya dai ta taka rawa matika kan bin kadin hakkokin wadannan al'ummomi. Wannan matsayi dai da aka kai na yaddar da kamfanin na Shell yayi na aikata laifin barin danyen man ya malala ya kuma gurbata muhallin al'ummomin na Bodo a Shiyyar Ogoni da ke yankin Nija Delta, tare kuma da amincewar biyansu diyya nasara ce babba da ba a tsammaci samunta ba nan kusa. Kimanin shekaru Shida ke nan da al'ummar ta Bodo suka shigar da kara a gaban wata kotu a London suna masu cewar malalar danyan man ta kassara muhallinsu tare da dukkanin hanyoyin rayuwarsu, wadda kuma sulhun da kotun ta London ta yi, ya kai ga matsayin da ake a yanzu na biyan diyyar ga al'ummar ta Bodo.