Gurɓacewar muhalli a Tunisiya
May 9, 2013A Tunisiya yanzu haka wata taɓargaza ta sinadarin guba da wani kamfani dake yin taki zamani da kuma harhaɗa wasu magungunan kashe kwari da kuma wanke karafa na gorar ruwa wato Aluminium da darma, wanda ya kan zubar da dagolon sharar gubar a cikin teku, ya janyo babbar illa ga masu aikin kamun kifi da noma da kiwo tare kuma da haddasa gurɓacewar muhali.
A saboda haka ruwan tekun kasar ya gurbace sakamakon gubar dake tarara a cikinsa.
"Wannan ruwan gubar dake tsiyaya ke nan a cikin ruwan teku na garin Gabes dake gabar tekun, a kudancin Tunisiyar inda ke da wani katafaran kamfanin gwamnati dake yin aikace aikce na tace karafa da kuma harhaɗa wasu sinadaran."
Zaman kashe wando ya addabi mazauna Gabes
Kasar ta Tunisiya wacce bata da ma'adinan karkashin kasa masu yawa ta mallaki sinadarin phosphat wanda da shi ake kaddamar da manyan ayyukan bincken kimiyya, abinda ya sa a yau a wannan gari na Gabes dake bakin tekun al'amuran noma da kiwo da kuma kamun kifin suka ja da baya sakamakon ruwan gubar dake zuba cikin tekun, wadda jama'a ke yin amfanin da ruwan domin yin ayyukan gona.
Mondher wani mazaunin bakin gabar tekun ne a garin Gabes daya daga cikin wakilai na kungiyoyi masu fafutukar kare muhalli.
"A da muna yara masunta ba sai sun yi nisa suke kama kifi ba, muna wanka tare da kifaye sannan ga gonaki dake daf da bakin tekun ana yin noma, abun gwanin kyau, amma yau dukkan wannan ya kau."
Wannan al'amari dai na sinadaran gubar kwararru sun yi gargadin cewar yana tattare da babbar barazana da al'ummar yankin, kana kuma suna iya fuskantar hayakin R"adio Activite" inda har ba a gusa jama'ar daga gurin ba tare da wanke gubar da ta kwarara a kasa da kuma cikin ruwan ba.
Nuridine Trabelsi shi ne daraktan kula da muhalli na yanki cewa yayi:
"Tabbas ba za mu boye muku ba muna da babbar matsala ta gurbacewar muhalli tun shekaru da dama kafin ma juyin juya hali. Mun yi wani shiri na sake fasalin kamfanonin. To amma aikin ne yake da wahala sannan gwamnati ba ta ba mu izini ba. To amma yanzu muna da kyakyawar niyya kuma ba za mu bari wannan dama ta sulbe mana ba."
Yawan mutanen dake mutuwa na karuwa
Yawan cututtuka da ake fama da su a wannan yanki irin su Athma da ciwon daji da sauran cutuka da suka shafi fatar jiki suna da nasaba ne da sinadarin gubar wanda ke ƙara adadin mutane da ke mutuwa a kowa ce shekara.
Moniya Guiza daraktar kula da fasahar kimiyya a jami'ar Gabes ta ce tilas ne a sararama ruwan tekun:
"Ina tsammani bai kamata ba a ci-gaba yi wa jama'a yau da gobe, barnar ta yi yawa, ya na da muhimmanci mu bar ma 'ya'yanmu da jikokinmu tsabtataccen ruwan teku domin babban arziki ne".
Mawallafa: Alexander Göbel / Abdurrahmane Hassane
Edita: Mohammad Nasiru Awal