1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin yarda na barazana ga hadin kan duniya

Abdullahi Tanko Bala
September 25, 2018

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yace rashin aminci da yarda a tsakanin kasashe na yin barazana ga hadin kan duniya.

https://p.dw.com/p/35TqK
Antonio Guterres
Hoto: picture-alliance/AP Images/R. Drew

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres a wannan Talatar ya bude taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya tare da kashedi da babbar murya game da karuwar rudani da rashin yarda a tsakanin kasashe wanda yace yana barazana ga hadin kan duniya.

Da yake jawabi ga zauren Majalisar Antonio Guterres yace rashin aminci a tsakanin kasashe ya sa lamura cikin mawuyacin hali.

Sai dai kuma bai ambaci wani ko kuma zargin wani bangare ba.

Guterres ya kuma yi amfani da wannan dama inda ya kara yin kira game da barazanar da duniya ke fuskanta game da sauyin yanayi. Yana mai cewa sauyin yanayi na faruwa cikin gaggawa fiye da yadda ake tsammani.