1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwagwarmayar kama madafun mulki a Senegal

January 30, 2012

Ana fama da tashintashina a ƙasar Senegal bayan da kotun tsarin mulki ta yanke ƙudurin ba wa Abdoulaye Wade damar tsayawa takara karo na uku a zaɓen da aka shirya gudanarwa watan Fabrairu.

https://p.dw.com/p/13t7o
Rapper Fou Malade, a member of the 'Y en a marre' (Enough is Enough) opposition group, addresses protestors during an opposition rally demanding that Senegalese leader Abdoulaye Wade renounce his bid for a third presidential term, at Place de l'Obelisque in Dakar, Senegal Saturday, July 23, 2011. Near him, a protestor holds a sign reading in French 'And you, do you have your electoral card? Enough is enough.' The protest marks the one-month anniversary of the massive June 23 demonstration which was the country's largest in recent memory and which emboldened the opposition, raising hopes that an Arab Spring-style democracy movement could spread south to sub-Saharan countries.(ddp images/AP Photo/Rebecca Blackwell)
Masu zanga-zanga a DakarHoto: AP

An fuskanci mummunar arangama tsakanin jami'an tsaro da suka yi amfani da barkonon tsofuwa da kuma masu zanga-zanga dake jifa da duwarwatsu da ƙone-ƙonen tayoyin mota a fadar mulkin ƙasar Senegal ta Dakar tsawon ƙarshen makon da ya wuce, sakamakon shawarar da kotun ƙoli ta ƙasar ta yanke na ba wa shugaba Abdoulaye Wade, mai shekaru tamanin da biyar da haifuwa, damar sake shiga takarar zaɓe, duk kuwa da cewar daftarin tsarin mulkin ƙasar. Dalilin da alƙalan suka bayar game da wannan shawara da suka yanke shi ne, wai lokacin da aka tsayar da ƙudurin ƙayyade wa'adin mulkin sau biyu kacal, tuni Abdoulaye Wade ya kama ofishinsa na shugabanci, kuma a saboda haka ba za a saka wa'adin na farko a cikin lissafi ba. Bisa ga ra'ayin shahararren mawaƙin ƙasar Senegal Youssou N'Dour, wanda kotun ta ƙolin dake bitar daftarin tsarin mulkin ƙasar ta sa ƙafa tayi fatali da buƙatarsa ta tsayawa takara domin ƙalubalantar shugaba Wade, wannan ƙuduri da kotun ta zartar babbar taɓargaza ce ga ƙasar Senegal. Dalilin da kotun ƙolin ta bayar game da haramta masa shiga zaɓen dai shi ne, wai bai gabatar mata da takardun dake nuna cewar yana da isassun magoya baya ba. Hakan dai abu ne da ya fusatar da shahararren mawaƙin:

Senegalese singer and songwriter Youssou N'Dour smiles during an interview in Dakar, capital of Senegal, July 2, 2001. The two-time Grammy nominee begins an eight-city U.S. and Canadian tour July 17, which will include an appearance on the David Letterman show and a live PBS broadcast from New York's Lincoln Center July 19. (AP Photo/Christine Nesbitt)
Youssou N'Dour, shahararren mawaƙin SenegalHoto: AP

"Wannan wata manufa ce ta siyasa kawai! Lokacin zantuttuka na fatar baki ya wuce, wajibi ne mu ɗauki matakai bisa manufa. 'Yan ƙasar Senegal dake goyan bayana ba zasu yarda a yi musu murɗiya ba. Kuma ko da yake ba na ƙaunar tashin hankali, amma fa ba ni da wani iko akan magoya-baya na."

A tashintashinar ta ƙarshen mako an kashe wani an sanda aya lokacin da matasa masu zanga-zanga suka tsayar da ƙudurin saka ƙafar wando ɗaya da jami'an tsaro da ƙone-ƙonen motoci da kantuna da ma tayoyi da kuma toszhe manyan hanyoyin mota a birnin Dakar. A kuma halin da ake ciki yanzun 'yan hamayyar ƙasar ta Senegal da sauran ƙungiyoyin farar hula sun haɗa kansu ƙarƙashin tutar wata ƙungiyar da suka kira, wai ta 23 ga watan yuni, bisa manufar hana shugaba Wade damar ta zarcen da yake fafutukar yi. An saurara daga ɗaya mawaƙin na zamani dake cikin rukunin 'yan hamayyar mai suna Thiat yana mai bayyana takaicinsa da cewar:

"Wani tsofo ne da ya maƙe kan kujerar mulki kamar kaska, daidai da da yawa daga cikin shuagabannin Afirka. A zamanin baya yana daga cikin masu ƙorafin haka, amma sai ga shi ma ya fuskanci irin wannan alƙibla. Senegal zata koma ƙarƙashin tsantsar kama-karya."

A nasa ɓangaren, a cikin wata hira da tashar telebijin ta France 24 tayi da shi, ya bayyana mamakin ƙyamar tsayawarsa takara da ake yi:

Senegal's President Abdoulaye Wade, 80, waits to address supporters at a re-election campaign rally in the city of his birth, Kebemer, Senegal, Monday 12 February 2007. Wade, who has held the presidency since 2000, is seeking a second term in a general election against 14 other candidates scheduled for February 25. EPA/Rick Valenzuela +++(c) dpa - Report+++
Shugaba Abdoulaye Wade na SenegalHoto: PA/dpa

"Zan kutsa filin daga ne ba tare da abokan gaba ba. Waɗannan mutanen ba su da wani muhimmanci. Tun shekaru biyu da suka wuce 'yan hamayya ke fafutukar ganin ban sake tsayawa takara ba. Hakan abin mamaki ne, saboda muna cikin wata janhuriya ce ta demokraɗiyya. Kowa na da ikon tsayawa takara idan har daftarin tsarin mulki ya amince. Amma ƙoƙarin waɗannan mutanen shi su hana wani tsayawa takara. Shin haka ake demokraɗiyya?"

Ko da yake 'yan hamayyar sun ce zasu ɗaukaka ƙara akan hukuncin na kotun ƙoli. Amma kuma ala-ayyi-halin sun ce zasu dakatar da takarar ta shugaba Wade ko ta halin ƙaƙa. Tuni Amirka ta farra bayyana damuwarta game da halin da ake ciki a Senegal, inda ta ce fafutzukar sakeb tsayawa takara da Abdoulaye Wade ke yi ka iya zama barazana ga zaman lafiyar ƙasar.

Mawallafi: Marc Dugge/Ahmad Tijani Lawal

Edita:Umaru Aliyu