1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Riek Machar ya karbi mukami a Sudan ta Kudu

Gazali Abdou TasawaFebruary 12, 2016

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya sake nada abokin hamayyarsa Riek Machar madugun 'yan tawayen kasar a kan mukamin mataimakin shugaban kasa

https://p.dw.com/p/1HuQr
Südsudan Salva Kiir Mayardit und Riek Machar
Hoto: Getty Images/AFP

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya sake nada abokin hamayyarsa Riek Machar a kan mukamin mataimakin shugaban kasa. Shugaba Kiir ya dauki wannan mataki na nada madugun 'yan tawayen kasar a cikin wani kudirin doka da ya dauka a jiya Alhamis.

Wannan nadi na a matsayin wani mataki na soma aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar da bangarorin biyu suka cimma a watan Agustan da ya gabata wacce ta tanadi tsagaita wuta da raba madafun iko, da nufin kawo karshen yakin basasa da kasar take fama da shi yau tsawon shekaru biyu.

Dama dai a baya Riek Machar ya taba rike wannan mukamin tsakanin shekara ta 2005 zuwa watan Yulin shekara ta 2013 lokacin da Shugaba Kiir ya tsige shi daga kan mukamin, abin da ya sake jefa kasar cikin yakin basasa.