1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sudan ta cimma yarjejeniya da Isra'ila

Ramatu Garba Baba
October 23, 2020

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya soki Sudan bisa amincewar da ta yi da Isra'ila a matsayin abokiyar hulda. A wannan Juma'ar ce kasashen biyu suka kulla yarjejeniyar dawo da dangantaka a karkashin jagorancin Amirka.

https://p.dw.com/p/3kN0I
Bildkombo Benjamin Netanyahu, Abdel Fattah al-Burhan, Donald Trump

Isra'ila da Sudan sun amince su dawo da hulda a tsakaninsu. An dai cimma wannan matsaya a sakamakon shiga tsakani da Amirka ta yi a wannan Juma'a. Shugaba Donald Trump ya kasance a zaman da aka yi ta wayar da tarho da Firai Ministan Isra'ila Benyamin Netanyahu da takwaransa na Sudan Abdallah Hamdok a kulla yarjejeniyar.

Kasashen biyu sun cimma matsaya kan batun inganta tattalin arziki inda suka amince su soma da bude kafar hada-hadar kasuwanci a tsakaninsu. Cikin watan jiya ne Kasashen Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa, suka dawo da dangantaka tsakaninsu da Isra'ila.

Daman shugaban na Amirka ya ce wani sharadin soke sunan Sudan daga jerin kasashen, shi ne ta amince da dawo da hulda da Isra'ila tare da biyan diyya ga wasu Amirkawa da hare-haren ta'addanci ya rutsa da su a shekara ta 1998 a Sudan.