Bunkasa lantarki a Tanzaniya
January 16, 2017Talla
Gwamnatin kasar Tanzaniya ta bukaci samun rancen kimanin dala milyan 200 daga Bankin Duniya don farfado da harkokin samar da wutar lantarki da ke cikin mawuyacin hali a kasar, kamar yadda ma'aikatar kula da makamashi ta tabbatar.
Shugaba John Magufuli, na bukatar ganin kasar ta Tanzaniya ta samu wadatacciyar wutar lantarki cikin farashi mai sauki domin bunkasa masana'antu, kuma yana ganin Bankin Duniya zai iya taimakawa matuka.