SiyasaArewacin Amurka
Trump ya ba Biden damar fara shirin karbar mulki
November 24, 2020Talla
A cikin wata wasika da Emily Murphy shugabar hukumar ta GSA ta aike wa da Joe Biden, ta ce ta bayar da wannan umurni bisa la'akari da dokokin Amirka kuma babu wanda ya yi mata katsalandan.
Wannan dai shi ne karon farko da gwamnatin Amirka ta sanar da amincewarta da nasarar Joe Biden makonni biyu bayan ya yi wa Donald Trump kyakkyawan kaye a zaben shugaban kasar da aka gudanar. A yanzu ke nan za a sakarwa Zababben Shugaba Joe Biden da shi da mukarrabansa kudin gwamnati domin shirya karbar gwamnati. Sai dai har yanzu shi Shugaba Donald Trump bai fito bainar jama'a ya amince da ya sha kaye ba.