1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Gwanin wanka na Kenya

Abdul-raheem Hassan
November 24, 2020

A kasar Kenya, an samu wani gwanin iya kwalliya na komai dozin. Mutumin mai suna Maina mwangi yana tinkahon ba wanda zai darashi iya daukar wanka.

https://p.dw.com/p/3lkg9
Kenia Nairobi | Maina Mwangi
Hoto: Andrew Wasike/DW

Maina Mwangi yana da shekaru 59, yana aikin kula da zirga-zirgar motocin safa, yana kuma lura da bukatun mataimaka direbobi da direbobin kansu. Sai dai wani abun da ke daukar hankali ga Mwangi shi ne, yadda yake zuwa aiki da kaya anko kama daga rigar Suit, takalma, igiyar wuya da rigar waya da zobe da agogo hatta safa da takunkumi da lema da alkalamin rubutu.

"Ina da rigunan suit 160, sama da takalma 200 da huluna 300 da saura. Mazan Kenya suna kwalliya ne kawai da bakin suit da kore. Wadannan sune aka saba da su a Kenya. Amma Allah ya ba ni baiwa da hikimar sanin launukan kaya da zan saka na fita dabam da sauran mutane, a haka na fara. Mutane ba su fahimci abin da nake yi ba a wancan lokaci, amma suna cewa ina fita tsab. Sannu a hankali suna karbar dabar yadda ya dace maza su yi kwalliya cikin launuka masu yawa."

Kenia Nairobi | Maina Mwangi
Maina Mwangi gwanin kwalliya na KenyaHoto: Andrew Wasike/DW

Mwangi ya tara tulin kaya cikin launuka dabam-dabam. Amma ba kullum Mwangi yake cikin kwalliya ba, domin kuwa da riga kala daya tak da yake addu'a domin rokon Allah ya ba shi kaya masu yawa.

A baya dai Mwangi yana sanya kayan gwanjo ne, amma a yanzu kayan da yake sawa yana kai darajar Euro 90 zu 750. Ya mallaki kaya da yake samu a matsayin kyauta daga masoyansa daga sassan duniya, har ta kantunan kaya a Nairobi na ba shi kyautar kaya.