A farko dai jaridar Neues Deutschland, ta bankado irin rawar da gwamnatin Birtaniya ta taka wajen hana a saka wa Najeriya takunkumin sayar dai mai, a zamanin mulkin marigaye janar Sani Abacha. Jaridar ta ce, Firaministan Birtaniya na lokacin, John Major ya yi duk mai yiwuwa wajen hana takunkumin da aka so a saka wa Najeriya. Musamman bayan kisan dan fafufutikar Niger Delta Ken Saro-Wiwa, kasashen duniya da kungiyoyin fafufutika sun tashi haikan don ganin an ladabtar da gwamnatin Sani Abacha. A cewar jaridar wasu takardu da aka bankado suna cewa tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Nelson Mandela, kwanaki biyar bayan kisan Saro-Wiwa, ya rubuta wa kasashen yamma da su dau matakin aza takunkumi kan shugaba Abacha, da kuma harkokin man Najeriya, to amma Birtaniya da sauran kamfanonin hakar mai suka datse wannan shirin da bukatar Mandela.
Ita ma jaridar Kölner Stadt-Anzeiger ta ce kasar Rwanda da ba a kasafe ake sakata cikin lissafi ba, in ba ana batun tuna wa da yakin kabilancin da ya hallaka mutane kimanin 8000 ba, to kasar yanzu dai, tana cikin kasashen da suka fi saurin samun bunkasar tattalin arziki a nahiyar ta Afirka. Bayan shekaru 20 da yakin rashin imani, a yanzu Ruwanda na neman zama babban misali a Afirka. Inda aka tabbatar cewa tsakanin shekara 2001 izuwa 2015, Ruwanda ta samu bukasar kudin shiga har kashi takwas cikin dari, wannan kuwa karuwa ce ta bangaren kudin shiga, na kayan da ake sarrafawa na cikin gida. Yanzu ma dai Kigali babbar birnin kasar ta kasance kusan wurin da ke zama cibiyar hada-hada a Afirka.
Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung, ta yi nazari ne kan badakalar cin hanci a kasar Angola, inda wani shafi da aka sani da Luanda Leaks, wanda ya ke zegunta almundahanar da 'yar tsohon shugaban kasar Angola Isabel dos Santos ta yi. 'Yan jarida dai na cikin wadanda suka fara tsegunta labarin, abin da ya kai ga mutane irin su Rui Pinto 'dan kasar Portugal kafa wata kungiya don kare masu tsegunta labari daga kasashen Afirka. A bisa tseguntawar da aka yi dai, an bayyana yadda 'yar tsohon shugaban kasar ta Angola ta yi amfani da mukamin babanta wajen azurta kanta, kuma a yanzu ma dai Isabel dos Santos, ita ce ta fi ko wacce mace yawan dukiya a nahiyar Afirka.
Yakin neman zabe na neman zama wani fagen daga a kasar Uganda, wannan shi ne labarin jaridar die tageszeitung. Jaridar ta bada bayanin abin da ya faru a garin Kasangati, da ke wajen Kampala, babban birnin kasar, bisa ga 'yan adawa masu goyon bayan mawakin da ya tsunduma cikin siyasa, wato Bobi Wine, yadda jami'an tsaro suka fara cilla musu hayaki mai sa hawaye, inda nan take wajen ya tirnike. Jaridar ta ce wannan matakin na jami'an tsaron Yuganda ya shafi matafiya da 'yan jarida, da mazauna kauyen da babu ruwansu, inda kowa ya kama tari, wasu har da mutuwa. Hakan ya nuna irin yadda shugaba Museveni ya ke kokarin kare kujerarsa ko da karfin bindiga.