Hadakar ma'aikata: Gidajen rediyo a Kenya na kokarin samar da daidaito
Sabon shirin tabbatar da adalci a tsakanin kowanne jinsi a ma'aikatu. Kenya ta zama zakarar gwajin dafi a fannin tsaga aiki a tsakanin maza da mata.
Mai gabatar da shirin rediyon Sky FM Irene Olwande
Gidajen rediyon Sky FM dana Lake Victoria a Kenya, sune suka soma bijiro da tsarin bai wa mata da maza dama guda wajen gabatar da shiri. A cewar Irene mai gabatar da shiri a gidan rediyon Sky FM, kowa zai ci gajiyar tsarin domin ba wanda za a bari a baya.
Hada aiki da kuma kulawa da iyali
Cikin hanzari Irene Olwande ke rugawa aiki domin gabatar da shiri, a sakamakon nauyin kulawa da iyali, a wasu lokuta tana fuskantar kalubale musanman fannin kulawa da yaran, da ke da bukatu dabam-dabam, kama daga na zuwa ganin likita ya zuwa makaranta, amma yanzu ana sassauta mata wajen ba ta zabin lokacin yin aiki, haka ma maza na samun wannan damar.
Mata masu goyo sun daina fuskantar barazanar rasa aikinsu
A kasar Kenya, kulawa da yara kaco-kam aikin mata ne, a sakamakon hakan, matan da suka yi karatu da ke kuma aikin gwamnati na fuskantar matsaloli. Amma yanzu da wannan sabon tsarin, ana bai wa iyaye mata da maza hutun haihuwa. Irene na matukar farin ciki da tsarin, yanzu ba ta fargabar rasa aikinta.
Matashiya da tayi zarra a tsakanin abokan aiki
An amince wa 'yar jarida Irene Olwande ta zo aiki da jaririnta, duk da cewa hakan ma na tattare da wasu kalubale, amma hankalinta a kwance, saboda tana da damar kulawa da jinjirin da kanta ba tare da neman taimakon wani ko wata ba, sannan sauran abokan aikinta sun nuna fahimta ba tare da yin korafi ba. Baya ga haka an tanadar ma iyaye masu goyo, dakin shayar da yara.
An shirya hadakar domin samar da daidaiton jinsi
Tsarin tabbatar da daidaito a tsakanin mata da maza 'yan jarida, ya shimfida matakin yin raba daidai, kama daga matakin daukar ma'aikata ya zuwa biyan albashi da sauransu. Har wa yau, aikin zai fi kyau, inda kowanne bangaren ke iya bayar da gudumowa, kafin daga bisani a yi nazari a kuma cimma matsaya in ji Olwande.
Jael Lieta, shugabar sashen gabatar da shirye-shirye a gidan rediyon Sky FM
DW Akademie tana aiki da tashoshi abokan huldar DW akalla 13 a kasar Kenya, domin aiwatar da wannan sabon tsarin. Jael Lieta ta kasance mace daya tilo da ke da babban mukami a tashar Sky FM. Ta ce, a matsayinta na mace, akwai kalubalen da take yawan cin karo da su, amma daga karshe, nasarorin da take samu daga sakamakon aiyukanta, na matukar faranta mata rai.
Kulawa da kare ma'aikata mata daga cin zarafi
Tsarin bai amince ko kadan da cin zarafi ko cin zalin mata ba. Ana son ganin ma'aikatu sun dauki nauyin kare mata ma'aikata daga cin zarafi koda a tsakanin takwarorinsu maza tare da kare rayuwa da lafiyarsu, gidan rediyon Sky FM na daukar nauyin kulawa da ma'aikatan mata da mahinmanci.
Gidajen rediyo da dama suna mayar da hankali kan tsarin samar da daidaito
Tare da goyon bayan Sashen DW Akademie, gidajen rediyon Sky FM da Radio Lake Victoria suka soma aiwatar da tsarin bai wa mata da maza daidaito a wuraren aiki, sun kuma yi hakan ne a shirye-shirye da suke watsawa.Tuni sauran tashoshi suka soma koyi da su. Hakarsu ta cimma ruwa, ganin yadda da dama suka amince cewa, sai da wannan hadakar, za a gudu tare a kuma tsira tare.