Jirgin saman kasar Senegal ya yi hadari
September 6, 2015Talla
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Sanegal ta sanar da cewa jirgin mallakar wani kamfani mai zaman kansa na kasar ya taso ne daga Ouagadougou na kasar Burkina Faso kuma ya bace an daina jin duriyarsa tun a yammacin wannan Asabar da misalin karfe bakwai agogon GMT a yayin da yake kimanin nisan kilomita 111 da yammacin Dakar babban birnin kasar ta Senegal. Tuni dai dakarun sojojin sama na kasar ta Senegal suka isa inda ake kyautata zaton jirgin ya fadi domin gudanar da bincike.