Hali mawuyaci na rayuwa a Gaza
July 21, 2014A daidai lokacin da lamura suke dada kazanta a dangane da irin lugudan wuta da sojojin Isra'ila ke yi a Zirin Gaza, al'ummar yankin na ci gaba da dogaro tare da kira ga duniya baki daya a kan ta sa baki wajen kawo karshen wannan tabargaza da ke gudana wanda kuma ke lamushe rayukan musamman na yara kanana da mata a wannan yanki.
Ana kwatanta yankin da kasancewa budadden gidan kurkuku mafi girma a duniya. Tsayinsa ya kai Kilomita 38 da fadi tsakanin Kilomita 6 zuwa 13. Girman Zirin Gaza bai shige rabin birnin Hamburg da ke Jamus ba, sai dai yana dauke da yawan mutane kusan daidai da na wannan birni mafi girma na biyu da ke yankin arewacin Jamus. A dan tsukin wuri na Gazan dai, akwai mutane kimanin miliyan guda da dubu 800, kashi 43 daga cikin 100 na wadannan mutane matasa da shekarunsu basu kai 14 da haihuwa ba, wadanda za a iya cewar tamkar an yanke su ne daga sauran sassan duniya. Khouloud Daibes, ita ce jakadar Falasdinawa a nan Jamus wadda ta yi bayanin mawuyacin hali da al'ummar kasarta ke ciki:
Ta ce"basu da ikon yin su, basu da aikin yi, kazalika basu isa su bar wannan yankin ba, suna rayuwa ne tamkar a cikin wani keji. Suna muradin samun kyakkyawar makoma".
Sai dai wannan fata nasu a kullum dada dusashewa yake. Tun bayan da Isra'ila ta kaddamar da wannan somame nata kusan makonni biyu da suka gabata, sama da Faladinawa 300 ne suka rasa rayukansu, baya ga wasu sama da dubu biyu da suka jikkata, daga cikinsu kuwa har da kananan yara masu yawa. Lamarin ya kara kazancewa tun bayan da dakarun Israela suka fara kai somame ta kasa, wanda ke da nufin lalata bututun Hamas.
'Yan Hamas dai su ne ke da madafan ikon Gaza. Sabanin yanayi da aka saba gani a baya, shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas na Kungiyar Fatah mai sassaucin ra'ayi, bai soki hare haren rokoki da 'yan Hamas ke yi a kan Bani Yahudun ba. Kuma Hamas na ci gaba da harba rokokin nata zuwa yankuna Israela babu kakkautawa, wanda kawo yanzu ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hular Bani Yahudun biyu.
A bangaran al'ummar Falasdinawan dai tamkar babu wurin gudu balle buya a Gaza. Duk da cewar sojin Israela kan yi gargadi kafin su fara lugudan wuta, ana fama da matsalar karancin kayan jinya wa jama'a. Abdallah Frangi shi ne gwamnan Gaza.
"Asibitoci na fama da karancin kayyakin aiki, babu gadaje, ga matsalar rashin wutar lantarki kusan ko wace sa'a, batu da ke dada haifar da matsala musamman ga marasa lafiya da ke bukatar tiyata".
Manazarta lamura da ka je su zo dai na ganin cewar, ya kamata a duba wannan batu da idon basira. Al'ummar Falasdinawan yanzu haka dai na fatan kasashen duniya da ke kallon halin da ake ciki a yankin na Gabas ta Tsakiya za su taimaka, wajen lalubo bakin zaren warware wannan matsala da ke ci gaba da ruruwa kamar wutar jeji.
Za a iya sauraron sauti daga kasa
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Muhammad Nasiru Awal