Sudan ta Kudu: Al'amura na rincabewa
July 30, 2016A wannan Lahadin ce ayyukan rundunar wanzar da zaman lafiyar ta Majalsair Dinkin Duniya a Sudan ta Kudun ke karewa, sai dai Kwamitin Sulhun ya amince da kara wa'adin aikin wanzar da zaman lafiyar zuwa nan da makwanni biyu. Da ta ke jawabi kan amincewa da kara wa'adin bayan kada kuri'a da mambobin kwamitin suka yi, jakadar Amirka a Majalisar Dinkin Duniya Samantha Power cewa ta yi:
"Dole ne mu fahimci halin da ake ciki a kasar a yanzu. Kada mu yi tunanin muna da sauran lokaci, bamu da shi kwata-kwata. Dole ne mu dauki mataki cikin gaggawa. Abin da ke faruwa yanzu haka a Sudan ta Kudu na nuni da cewa al'amura ka iya rincabewa duba da yadda rikicin ke saurin yaduwa a sasan kasar da kuma mummunan halin da al'umma ka iya tsintar kansu a ciki."
Kimanin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya dubu 12 ne dai ke aikin kare rayukan fararen hula a Sudan ta Kudun, jaririyar kasar ta duniya da tun da ta samu 'yancin kanta a shekaru biyar din a suka gabata ta ke fama da rikici da aka kiyasta ya lashe rayukan akalla mutane 300.