1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Madugun 'yan adawa ya koma gida

Mahaman Kanta AMA
November 15, 2019

Jagoran gungun 'yan adawa ya koma a gida bayan shafe tsawon shekaru yana gudun hijira biyo byan tuhumarsa da aikata laifin safarar jarirai daga Najeriya, zargin da ya kai shi ga zama gidan yari a Jamhuriyar Nijar.

https://p.dw.com/p/3T7W8
Hama Amadou
Hoto: DW/S. Boukari

Ana dab da karshen wannan makon ne ba zato ba tsammani madugun 'yan adawar Nijar Hama Amadou ya sauka a filin jirgin saman na birnin Niamey, kai tsaye madugun 'yan adawar da ya shafe tsawo shekaru kusan hudu yana gudun hijira ya isa a makabarta don yi addu'o'i ga mahaifiyarsa da ta cika a makwannin da suka wuce, tare da rakiyar dimbin magoya bayansa da suka masa rakiya.

Dawowar tsohon shugaban majalisar dokoki kuma madugun 'yan adawar Malam Hama Amadou bata rasa nasaba da zaman  makoki da ya soma ne biyo bayan rashuwar mahifiyarsa, kana kuma ya share daya baya rasa nasaba da halin da kasar take ciki kan batun sulhunta rikicin siyasar kasar da ya ki ci yaki cinyewa, wanda kuma tuni bangarorin da basa ga maciji suka soma tattaunawa akai.

Makomar Hama Amadou a fagen siyasa.'Yan siyasa da dama na kallon dawowar shugaban a matsayin wata kada da za ta taimakawa wajen yi masa ahuwa game da zargin safarar jaririai da ake tuhumarsa akai wanda a baya wata kotu ta hukunta shi, duk da daukaka karar da ya yi kotun ECOWAS ta yi watsi da bukatar wankesa daga aikata laifin, batun da kuma ke zamewa madugun na 'yan adawa wani karfen kafa.

Wahlplakat für Hama Amadou Niger
Hoto: DW/M.Kanta

Masanan dokoki na yiwa batun wani sharhi na daban, inda suke cewa yana da hurumin kai kanshi a gaban shari'a muddin shugaban kasa bai dauki wani mataki na yin ahuwa ga madugun 'yan adawar ba, ko kuwa ma a kotu ta dauki matkin zuwa nemansa a gida.

A yanzu dai hankali ya koma kan yadda za ta kasance a gaba, ko yi masa ahuwa kan kurakuran da ya aikata wadanda a baya yayi zaman gidan yari a ciki, ko kuwa sake komawarsa gidan yari domin kammala sauran watannin da suka rage a hukuncin da kotu ta yake masa na dauri a gidan kaso wanda ya fice daga cikinsa da kyar bisa yanayi na rashin lafiya.