1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hama ya yi taron magoya baya a Maradi

October 5, 2020

Siyasa ta fara daukar dumi a Jamhuriyar Nijar inda yan takara daga jam'iyyu daban daban sukae cigaba da taron gangami na magoya baya a cikin birane da karkara.

https://p.dw.com/p/3jSa3
Wahlplakat für Hama Amadou Niger
Hoto: DW/M.Kanta

Shugaban jam’iyyar Moden Lumana Hama Amadou ya samu gagarumar tarba daga magoya bayansa da suka fito daga birni da karakarar jihar Maradi inda ya yi musu jawabi a dandalin Tribune. Sai dai sabani irin jawabin da yayi a Tera da wasu ke cewa ya wuce gona da iri, a Maradi ya sassauta.

Shugaban adawar ya yi Magana game da koma bayan tattalin arziki da yace jihar Maradi dama kasar baki daya suke fuskanta, inda yayi alkawalin maido martabar Maradi kamar yadda aka santa a baya.

A nasa bangaren dan takarar jam’iyar PNDS Taraya malam Mohamed Bazum ya soma wani rangadi a cikin jihar Maradi a wannan litinin inda zai kai ziyara cikin karakara don ganawa da magoya bayansa.

A fili take dai siyasar Niger zta fara daukar zafi gabanin zabubukan dake tafe .