1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hamas ta kashe 'yan Isra'ila 15

Adamu Usman Salihu | Abdul-raheem Hassan
December 4, 2023

Akalla mutane 1,200 yawanci fararen hula ne suka mutu a rikicin Gaza da Isra'ila tun ranar bakwai ga watan Oktoban shekarar 2023. An kuma kama mutane da dama daga bangarorin guda biyu a matsayin garkuwa.

https://p.dw.com/p/4ZkxB
Sojojin Isra'ila sun kai farmaki a zirin GazaHoto: IDF/Xinhua/picture alliance

Ofishin Firaiministan Isra'ila Benjamin Netenyahu ya ce adadin mutanen da suka mutu daga cikin wadanda kungiyar Hamas ta yi garkuwa da su ya kai mutum 15.

Da yake tabbatar da sabbin alkaluman, ofishin ya ce akwai fararen hula mutane 11 daga cikin wadanda suka mutu, sannan akwai sojoji guda uku.

Kusan mutane 1,200 akasarinsu fararen hula suka mutu tun daga ranar bakwai ga watan Oktoba na shekarar 2023 bayan kungiyar Hamas ta kaddamar da hari kan Isra'ila, kungiyar ta kuma yi garkuwa da kusan mutane 240.

Ya zuwa yanzu an saki 'yan Isra'ila guda 80 da kuma Faladsinawa 240 da ke tsare a hannun Isra'ila, a wata yarjejeniya da kasar Katar ta shiga tsakanin bangarorin biyu da ke fada da juna a yankin Gabas ta Tsakiya.