Hamas ta sako karin mutanen da tayi garkuwa da su
November 26, 2023Talla
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya kai ziyararsa ta farko Zirin Gaza tun bayan da kasarsa ta kaddamar da yaki kan kungiyar Hamas a watan da ya gabta.
A wani jawabi da ya yi, shugaban ya bayyanawa sojojin kasarsa da ke yaki a Gaza din cewar ba za su tsaya ba har sai sun yi nasara, inda ya kara da cewar babu abin da zai tsayar da su domin suna da iko da karfi da ma jajircewar samun nasara.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da aka shiga rana ta 3 ta tsagaita wuta da musayar fursunoni 'yan Falasdinu da ke kurkukun Isra'ila da kuma 'yan Isra'ila da Hamas ke garkuwa da su