1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jinkirta sakin 'yan Isra'ila da Hamas ke garkuwa da su

Binta Aliyu Zurmi
November 25, 2023

Kungiyar Hamas ta sanar da jinkirta zagaye na biyu na sakin 'yan Isra'ila da take garkuwa da su a Gaza har sai mahukuntan Isra'ilan sun ba da damar shigar da kayayakin agaji a yankin arewacin Zirin.

https://p.dw.com/p/4ZRmu
Israel-Hamas agree on temporary truce
Hoto: Ibraheem Abu/REUTERS

Hamas ta kara da cewar mudin Isra'ila ba ta mutunta sharuddan yarjejeniyar sakin Falasdinawan da ke kurkukunta ba, to za ta ci gaba da rike wadanda ta yi garkuwa da su.

A jiya Juma'a ranar farko, an yi musayar Falasdinawa 39 da 'yan Isra'ila 13 da aka yi garkuwa da su, inda aka tabbatar da tuni sun koma cikin iyalansu.

Kazalika an kuma ‘yantar da ‘yan kasar Thailand 10 da dan Philippines daya daga Gaza kuma nan ba da jimawa ba za su koma gida.

Isra'ila dai ta sha alwashin komawa fagen yaki da zarar wa'adin da aka diba na tsagaita wuta ya cika har sai ta ga bayan mayakan na Hamas gabaki dayansu a cewar sanarwar da suka fidda.