1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hamas za ta bincika harin roka a Isra'ila

October 18, 2018

Jagrorin kungiyar Hamas sun ce zasu kaddamar da bincike kan wani harin da aka kai kan wani sashe na kasar Isra'ila.

https://p.dw.com/p/36nSm
Palästina Israelische Angriffe in Rafah
Hoto: picture-alliance/newscom/UPI Photo/I. Mohamad

Shugabannin kungiyar Hamas da ke a zirin Gaza, sun yi alkawarin kaddamar da bincike kan wani harin roka da aka kai kan wani sashe na Isra'ila, a wani abin da ake ganin kokari ne na kwantar da fargabar yaki tsakanin bangarorin biyu.

'Ya'yan Isra'ilawa wadanda ke kusa da kan iyaka da Falasdinu, sun koma makarantu, bayan rufe wajen da aka yi a jiya Laraba, bayan harin da aka kai birnin Beersheba.

Sai dai wasu na hasashen samun hare-hare na martani, saboda zargin da Isra'ailar ke yi wa kungiyar ta Hamas.

Kungiyar Hamas ta fitar da sanarwar nesanta kanta da harin, wanda wasu kananan yara uku suka tsallake rijiya da baya.

Firaministan Isra'ilar Benjamin Natanyahu ya ma jagoranci wanni taron majalisar tsaro da yammacin jiya Laraba, bayan harin.