Najeriya: Matakin ramawa kura aniyarta
December 13, 2021Wani sautin murya na ministan harkokin sufurin jiragen saman Najeriyar Hadi Sirika ne dai, ke shirin yamutsa lamura a tsakanin manyan kawayen a duniya baki daya. Kuma daga dukkan alamu rikicin annobar COVID-19 ne ke shirin rikida zuwa rikicin diplomassiyar, a tsakanin Tarayyar Najeriya da manyan kawayen nata Saudiyya da Ingila da ma kasar Kanada. Ministan dai ya ce daga Talatar wannan mako, Abujar tana shirin rama gayya kan matakin kasashen da a makon jiya suka ayyana dakatar da al'ummar Najeriyar shiga kasashensu sakamakon corona nau'in Omicron. Gwamnatin Najeriyar dai na shirin bayar da sanarwa, mai kama da aiken sako ga kasashen da kila ma wasu da ke shirin bin sahu a cikin rikicin sabon nau'in na corona.
Najeriyar dai daga dukkn alamu, na fatan aiken sako a cikin sabo na matakin da ministan ya ce yana da zummar kare martaba ta 'yan kasar a ko'ina a duniya. Matakin kuma da a cewar Dakta Hussaini Tukur Hassan da ke zaman masanin diplomassiya a jami'ar Keffi da ke jihar Nasarawa, bai saba da ka'ida ta huldar kasa da kasa ba. To sai dai kuma koma wace riba Najeriyar ke fatan samu a cikin sabon matakin dai, daga dukkan alamu rikicin na iya babban tasiri har ga tattalin arzikin kasar da ke da tasiri. Ko bayan hutun kirsimeti a Ingilar da ke zaman al'adar 'yan bokon Najeriyar, sake bude umara na daukar hankalin masu akwai cikin kasar a halin yanzu. Kuma a fadar Abdul'azeez Sabitu da ke zaman shugaban kamfanin Arafat Air Service kuma tsohon shugaban kungiyar masu tsara sufuri na sama a arewacin Najeriyar, tuni asarar ke kara yawa sakamakon tsayar da harkokin jirage a tsakanin Najeriyar da kasar Saudiyya. Warware rikicin a cikin gaggawa dai, na iya rage radadin da ke zaman tsumagiyar kan hanya fyade yaro fyade babba.