Har yanzu 'yan makaranta a Gaza ba su koma karatu ba
September 10, 2014Bayan yarjejeniyar tsagaita buɗe wutar da aka cimma tsakanin Hamas da Isra'ila har yanzu azuzzuwan da 'yan makaranata ke ɗaukar darasi a ciki suna ciki makil da 'yan gudun hijira waɗanda yaƙin da aka gwabza a ƙasar ya yi sanadiyyar rusa gidajensu baki ɗaya. Kimanin mutane dubu 50 suke zaune a cikin wurare na wucin gadi a ckin makarantun.
Duk da yarjejeyar da aka cimma har yanzu al'ammura ba su daidaita ba.
A wata makarantar ta Majalisar Ɗinkin Duniya da ke a yammacin Gaza wacce ke karɓar mutane kusan 1500 waɗanda suka guje daga gabashin Gaza akwai iyalai yara da manyan. Mayad Alud mai kimanin shekaru 12 ɗan makaranta ne da ke zaune a wurin.
'' An lalata gidajenmu shi ya sa muke nan, a cikin wannan makarantar. Abin da kuma ke hanna mana fara karatun ke'nan.''
Majalisar Ɗinikin Duniya ta ce hare-haren na dakarun Isra'ila sun shafi makarantu kimanin 216 kuma 22 daga cikinsu gaba ɗaya sun rushe. Kana da dama daga cikin iyayen yara da ma yan makarantar sun yanke ƙauna kan cewar a shekarar bana za a yi karatun.
Fatan 'yan makarantar na sake buɗe makarantu da gaggawa
To amma ita wannan 'yar makarantar mai shekaru goma mai sunan Fadila wacce ke sirin zuwa ajin gaba da sakandri ta ce tana sa ran kafin wani lokaci komai ya daidaita.
'Ina son makaranta,bara mun ji daɗi ina tunawa da abokanai na muna jiran a sake buɗe mana makarantun.''
ofishin ministan ilimi na Gaza ya ce ma 'yan gudun hjirar sun fice daga cikin makarantu to aƙalla sai an ɗauki mako guda kafin komai ya daidaita.