Hare-haren kunar bakin wake a Kudancin Iraki
May 1, 2016Talla
Bam na farko dai ya tashi ne kusa da cibiyar majalisar jihar, yayin da na biyu ya tashi kusa da inda motocin bus-bus ke tsaya wa kusa da inda na farkon ya tashi, inda ake ganin kungiyar ta IS dai ba ta saba kai irin wannan hari ba a wannan yanki.
Hakan na zuwa ne yayin da dubban masu zanga-zanga a yau Lahadi suka mamaye yankin nan da ke da babban tsaro na birnin Bagadaza inda manyan ma'aikatun gwamnati suke, bayan da a yammacin jiya suka mamaye majalisar dokokin kasar domin nuna kosawar su ga halayan 'yan siyasar kasar da suka kasa samun daidaito wajan kafa sabuwar gwamnatin mai muradin sauyi a kasa.