1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare haren sojojin Sudan a Sudan ta Kudu

November 11, 2011

Dangantaka tsakanin ƙasashen Sudan da maƙobciyarta Sudan ta kudu na ƙara rincaɓewa bayan wani harin da sojin Sudan suka kai akan wata cibiyar 'yan gudun hijira dake a Sudan ta kudu

https://p.dw.com/p/138qr
Wata cibiyar yan gudun a KurdufanHoto: AP

Amurika ta yi allah wadai da hare hare ta jiragen sama da sojojin ƙasar Sudan suka kai akan wani sansani 'yan gudun hijira na Yida da ke a Sudan ta kudu. A cikin wata sanarwa da kakakin fadar gwamnatin Amurkan ta White House Jay Carney ya bayyana ya ce sun buƙaci hukumomin Sudan ɗin da su dakatar da kai hare hare nan take.

Sansanin na 'yan gudun hijira na Yida wanda ke kan iyaka tsakanin ƙasahe biyu wanda kuma ke kumshe da 'yan gudu hijira dubu 20 ya sha ruwan bama bamai daga dakarun ƙasar Sudan;wani jamin gwamntin ya ce mutane guda12 suka mutu yayin da wasu guda 20 suka jikata; sai dai yazuwa yanzu babu wata majiya mai zaman kan ta da ta tabata da gaskiyar wannan addadi na mutuar jama'ar da aka samu.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou