Hare-haren Taliban a Pakistan
August 15, 2014Kungiyar Taliban reshen kasar Pakistan ta ce ita ce ke da alhakin kai wani hari da ya yi sanadiyyar mutuwar 'ya'yan kungiyar 12. Wasu gungun 'yan bindiga ne dai dauke da makamai da jigidar boma-bomai domin kai harin kunar bakin wake suka tinkari sansanin rundunar mayakan saman Pakistan din da ke Samungli da kuma sansanin sojoji na Khalid wanda dukkansu ke garin Quetta babban birnin gundumar Baluchistan. Bayan kwashe sama da sa'oi tara ana fafatwa tsakanin dakarun kasar ta Pakistan da kuma maharan, dakarun gwamnatin sun samu nasarar fatattakar maharan inda 12 daga cikinsu suka sheka barzahu. A baya-bayan nan dai kasar pakistan na fuskantar hare-haren ta'addanci daga kungiyar ta Taliban akai-akai.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu