Hari a kan 'yan yawan bude ido a Afganistan
August 4, 2016Talla
Wasu yan yawan bude ido na kasashen Birtaniya da Jamus da kuma Amirka su 12 wadanda suka je yawan shakatawa a Afganistan,Sun fada cikin wani tarko na kwantan bauna na 'yan Taliban a tsakanin garuruwan Bamyan da Herat da ke a yammacin Afganistan.Wani babban jami'in gwamnati na garin Heirat ya ce da dama daga cikin 'yan yawan biude ido sun samu raunika a sa'ilin da 'yan Taliban din suka harba roka a kan motarsu.