Wani sabon hari a birnin Khartoum ya hallaka gwamman mutane
June 17, 2023Talla
Harin wanda aka kai yankin nan na Yarmouk ya kuma lalata gidaje 25 duk a cewar sanarwar.
Can ma a yankin Darfur, ma'aikatan jinya na kokawa da yawan mutanen da ke jikkata a cigaba da kwabza kazamin fada da bangarorin da ke gaba da juna ke yi a kasar.
Adadin mutanen da suka rasu a yakin tun bayan barkewarsa a tsakiyar watan Afirilu ya haura mutum dubu 2.