Hari bam akan rijiyoyin man Sudan ta kudu
March 1, 2012ƙasar sudan ta kudu ta zargi takwararta kuma maƙobciyarta sudan da harba bama-bamai akan rijiyoyinta na fetur da ke kusa da iyakar waɗannan ƙasashen biyu da ke gaba da juna. Ministan watsa labaran Sudan ta kudu Barnaba Marial Benjamin da ya yi Allah wadai da abin da ya kira takalar fada ta sudan, ya ce bama-bamai sun lalata wata cibiya ta samar da ruwan sha ga kasarsa a Kodorfan ta kudu. Dama dai ƙasashen biyu na takaddama game da wannan yanki mai arzikin man fetur. Sudan da kuma sudan ta kudu na zargan junansu da ɗaure wa 'yan tawayen ƙasashen na su gindi da nufin haddasa rikici a cikinsu.
A nata ɓangaren kasar Amirka ta zargi shugaba Omar Hasan al-Bashir na Sudan da hanna ruwa gudu a ƙoƙarin da ake yi na tabbatar da zaman lafiya tsakanin ƙasarsa da kuma sudan ta kudu. sakatariyar harkokin wajen kasar ta Amirka wato Hilary clinton ta bayyana wa majalisun ƙasarsat cewar shugaban sudan na ƙoƙarin yin kafar ungulu ga yarjejeniyar sulhun da ƙasarsa ta kulla da Sudan ta Kudu.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Usman Shehu Usman