Hari kan asibiti a Yamen
January 10, 2016Harin wanda ya faru a yankin da 'yan tawaye suka fi karfi, ya yi sanadin rusa aksarin ginin asibitin. Dama can yankin da harin ya faru, ya sha samun hare-haren bama-bamai daga jiragen yakin Saudiyya. A cewar Raquel Ayora, daraktar gudanarwar ta kungiyar Doctors Without Boarders, asibitin sananne ne kuma duk masu yaki da juna babu wanda zai ce ba shi da masaniya inda suke bada agaji ga jama'a. A wannan harin dai mutane 10 suka jikkata, ko da yake ana kyautata zaton wadanda lamarin ya shafa za su karu. Wannan dai shi ne karo na uku a cikin watanni hudu da ake kai wa asibitocin kungiyar farmaki a kasar Yamen da yaki ya dai-daita. Kungiyar Doctors Without Boarders tana ci gaba da aikin bada agaji a jihohin takwas na kasar Yamen, duk kuwa da ficewar da kungiyoyin bada agaji daga Yamen ciki har da MDD, ta kwashe ma'aikatanta. Babu dai wanda ya dau alhakin harin da ya ruguza ginin asbitin kungiyar, amma sau da dama jiragen yakin Saudiyya suna yin luguden wuta a yankin, tun fara yin ruwan bama-bamai a kasar Yamen tun watanni 10 da suka gabata.