Hari kan jami'an tsaro a Burkina Faso
November 15, 2021Talla
Sai dai wasu jami'an tsaro sun ce adadin ya kai 30 kuma akwai yiwuwar ya karu, wanda ake gani shi ne hari mafi muni a kan 'yan sanda.
Harin da aka kaddamar da shi a ranar Lahadi, ya auku ne a wani wurin bincike na 'yan sanda da ke kusa da mahakar zinari a garin Inata da ke arewacin Burkina, wannan harin na zuwa ne kwanaki biyu bayan da wani makamancinshi ya kashe 'yan sanda bakwai a kan iyakokin Nijar da Mali.
'Yan ta'adda da suka yi mubaya'a da kungiyar al-Qaeda da ta IS sun jima suna aikata ta'asa a iyakokin kasashen Burkina Faso Nijar da Mali duk da sojojin kawance da na kasar Faransa da ke yankin.