Hari ya ritsa da Yahudawa a Birnin Kudus
February 10, 2023Talla
Wannan harin da 'yan sandan Isra'ila suka bayyana a matsayin na ta'addanci, ya faru ne a Ramot inda yawancin masu tsattsauran ra'ayi ke zaune a wuraren da Isra'ila ta mamaye. Dama dai ana fargabar barkewar tashin hankalin da ba za a iya shawo kansa ba sakamkon yadda rikicin Isra'ila da Falasdinu ke ci gaba da ruruwa tun farkon wannan shekara.
Ko makonni biyun da suka gabata ma, sai da wani Bafalasdine ya harbe wasu ‘yan Isra'ila shida da wata ‘yar kasar Ukraine har lahira a kusa da majami'ar unguwar Yahudawa da ke gabashin Birnin Kudus. kasashen duniya da dama sun yi kiraye-kiraye ga Isra'ila da 'yan yankin Falesdinu da su kwantar da hankulansu sakamakon karuwar tashe-tashen hankula.