An kai wani hari a Zimbabuwe
June 23, 2018Shugaba Emmerson Mnangagwa wanda ya fara gangamin yakin neman sake zabar sa a matsayin shugaban kasa, ya nunar da cewa harin da aka kai a yayin da yake gangamin, shi aka nufi kai wa sai dai lokacinsa bai yi ba. Mnangagwa ya kuma sanar a shafinsa na Twitter cewa ya ziyarci mutane da dama da harin ya rutsa da su. Ya kuma yi kira ga al'ummar kasar da su hada kawunansu, tare da jadda cewa za su dauki mataki domin dakile abin da ya bayyana da aikin matsorata da ba zai bari su yi tasiri ba yayin da suke kokarin gudanar da zabuka a ranar 30 ga watan Yuli ma zuwa. Kakakin Shugaba Mnangagwa George Charamba ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Jamus dpa cewa mataimakan shugaban kasar biyu Kembo Mohadi da Chiwenga sun samu raunuka sai dai tuni aka duba su a asibiti. Ya kara da cewa shi ma shugaban jam'iyyar Zanu PF Engelbert Rugeje ya samu raunuka. Garin Bulawayo dai na zaman garin da 'yan jam'iyyar adawa ta Movement for Democratic Change ke da rinjaye.