Bam ya kashe mutane a Libiya
May 25, 2018Talla
Hukumomin tsaro sun ce bam din ya tashi ne cikin wata mota kusa da babban Otal din Tibesti, inda musulmai ke gangamin bukukuwan murna a watan azumin Ramadana. Babu wata kungiya da ta dau alhakin harin, amma hukumomin Libiya na zargin 'yan ta'adda da aka ci karfinsu a yankin ne ke yunkurin maida martani. A baya dai sojoji sun sanar da nasarar kakkabe tungar kungiyoyin ta'adda da ke birnin na Benghazi, tare da ayyana karbe iko da birnin bayan shafe shekaru uku ana gwabza fada.