1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTimor ta Gabas

Harin Isra'ila ya salwantar da rayuka a kasar Syria

March 30, 2024

Wani hari da Isra'ila ta kaddamar ta sama a birnin Aleppo na kasar Syria, ya kashe akalla mutane ciki har da sojojin gwamnati 38 da ma wasu mayakan Hezbollah bakwai.

https://p.dw.com/p/4eH9u
Hari da aka kai kan birnin Aleppo na Syria
Hari da aka kai kan birnin Aleppo na SyriaHoto: Muhammed Sheekh/abaca/picture alliance

Sabon hari da Isra'ila ta kai ta sama a birnin Aleppo na Syria, ya salwantar da mutane 52 ciki har da sojojin gwamnati 38 da ma wasu mayakan Hezbollah bakwai.

Hari ne dai da Isra'ilar ta kai a kan cibiyar adana makaman roka mallakin 'yan Hezbollah da ke kusa da filin tashin jirage da ke birnin, kamar yadda kungiyar kare hakki ta Syrian Obervatory for Human Rights mai cibiya a Burtaniya ta tabbatar.

Alkaluman farko dai na wadanda suka salwanta a harin na Isra'ila da aka kai ranar Juma'a, mutum 44 kafin daga bisani suka karu zuwa mutum 52 a yau Asabar.

Hare-haren Isra'ila a Syria dai na karuwa a baya-bayan nan musamman tun bayan harin ranar bakwai ga watan Oktoba da kungiyar Hamas mai dasawa da Hezbollah.

Haka ma lamarin na hare-haren ramuwar gayya yake a Labanan, inda can ma ake da mayakan kungiyar ta Hezbollah.