Harin Isra'ila ya ta'azzara a Zirin Gaza
July 29, 2014Dakarun Isra'ilan dai sun dauki tsawon daren jiya suna kai harin bama-bamai a Zirin Gaza, wanda ke zama mafi munin harin da suka kai a wannan yanki makonni uku da kaddamar da wannan fada. Sababbin somamen Isra'ilan na zuwa ne, bayan da Fraiminista Benjamin Netanyahu ya yi gargadin yiwuwar tsawaita hare haren nasu a Gaza.Tuni dai babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yi kira da a gaggauta tsagaita wuta:
"Lokaci ya yi na tsagaita wuta ba tare da bata lokaci ba, domin kare rayukan al'umma. Sabo da halin da mutane suke ciki ya zamanto wajibi a tsayar da wannan fada. Wannan fada ya yi sanadiyyar rayukan Falasdinawa sama da 1,000, akasarinsu fararen hula, daruruwansu kuwa yara kanana. A daya hannun kuma harin rokokin Hamas ya yi sanadiyyar rayukan fararen hula uku na Bani Yahudu".
Tun a daren jiyan ne dai, sararin samaniyan Gaza ya turnuke da hayaki, sakamakon hare-haren dakarun na Isra'ila babu kakkautawa.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Usman Shehu Usman