Harin kunar bakin wake ya hallaka mutane da yawa
August 23, 2017Akalla mutane biyar aka kashe sannan wasu 42 suka samu raunika lokacin da wani dan kunar bakin wake ya ta da bam cikin wata mota a kusa da shalkwatar 'yan sandan lardin Helmand da ke kudancin kasar Afghanistan.
Shugaban rundunar 'yan sandan lardin Abdul Ghafar Safai ya fada wa kamfanin dillancin labarun Reuters cewa harin bam din ya rutsa da jami'an tsaro da suka je karbar albashinsu a babban birnin lardin Helmand wato Lashkar Gah.
Ya ce: "Jami'an rundunar sojojin Afghanistan sun hallara a gaban shalwakatr 'yan sanda don karbar albashinsu a wani reshen bankin Kabul, sai kawai aka ji karar fashewar bam a cikin mota. Amma yanzu mun shawo kan lamarin."
A watan Yuni da ya gabata ma dai 'yan Taliban sun kai hari kan jami'an tsaro da suka je karbar albashinsu a wani banki da ke a birnin na Lashkar Gah, lamarin da ya tilasta jami'ai kafa reshen bankin a harabar shalkwatar 'yan sandan.